IQNA

Kasashen Duniya sun yi  Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a hubbaren Shahcheragh a Shiraz

14:15 - August 15, 2023
Lambar Labari: 3489648
Tehran (IQNA) Harin ta'addancin da aka kai a wurin ibadar Shahcheragh da yammacin ranar Lahadi ya fuskanci tofin Allah tsine a yankin da ma duniya baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa MDD, kungiyar hadin kan kasashen musulmi, kasashen larabawa na mashigin tekun Fasha, Iraki, Siriya, Rasha da Oman sun yi Allah wadai da harin ta'addanci da ya afku a hubbaren Shahcheragh da ke birnin Shiraz na kasar Iran. sun kuma bayyana goyon bayansu ga gwamnati da al'ummar Iran

A yammacin Lahadin da ta gabata ne wani dan ta'adda dauke da makamai ya bude wuta a hubbaren Shahcheragh (AS) da ke Shiraz, kuma a wannan harin ta'addancin mutum daya ya yi shahada, wasu takwas kuma suka jikkata. Jiya da yamma kuma an sanar da cewa daya daga cikin wadanda suka jikkata ya mutu sakamakon munin raunin da ya samu.

Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar da kansu sun yi Allah wadai da harin da aka kai a wurin ibadar Shahcheragh a yammacin ranar Litinin. Kungiyar ta'addanci ta ISIS ta dauki alhakin wannan harin.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Bahrain ta kuma sanar a cikin wata sanarwa cewa, a ko da yaushe kasar tana yin Allah wadai da irin wannan danyen aikin.

Har ila yau ma'aikatar harkokin wajen kasar Kuwait ta fitar da wata sanarwa da kakkausar murya na yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai Shahcheragh (AS) tare da yin watsi da duk wani nau'in tashin hankali da ta'addanci gaba daya, tana mai jaddada muhimmancin daukar matakai tare da hadin gwiwar bangarori daban-daban don tinkarar ta'addanci da sakamakonsa. .

Shi ma babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi da ke birnin Jeddah na kasar Saudiyya Hossein Ebrahim Taha ya jajantawa gwamnatin Iran da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a wannan lamari.

Tarayyar Rasha ta kuma yi Allah wadai da wannan lamari a daren jiya a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin intanet na ma'aikatar harkokin wajen Rasha.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya kuma sanar da cewa: Antonio Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kakkausar suka kan harin ta'addancin da aka kai a Masallacin Shahcheragh.

Iraƙi dai ta yi Allah wadai da harin ta'addancin kafin wannan. A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Irakin ta fitar, an jaddada matsayin kasar na kin amincewa da ta'addanci a kowane nau'i da kuma irin matsayin kasar Iraki da kasashen duniya wajen tunkarar ta'addanci da goyon bayan duk wani kokari na alheri da nufin kawar da tsatsauran ra'ayi da tashin hankali.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Oman ta kuma bayyana jajenta da jajantawa gwamnati da al'ummar Iran ta hanyar buga wata sanarwa. A cikin wannan bayani an bayyana cewa, muna mika ta'aziyyarmu ga kasar amintacciyar kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma iyalan wadanda harin da aka kai a wurin ibadar Shah Cheragh da ke birnin Shiraz ya rutsa da su, kuma muna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. .

Har ila yau ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a hubbaren Shahcheragh da ke birnin Shiraz.

 

 

 

 

4162666

 

 

captcha